Jummaʼa 21 Agusta 2026 - 19:01
Ayatullah Bahjat: A Ranar 9 ga Rabi’ul Awwal, Idan da Gaske Kake Son Yi wa Ahlul-Baiti (A.S.) Hidima, Ka Yi Wannan 

Hauza/ Ranar 9 ga watan Rabi’ul Awwal na daga cikin ranakun da ake da ra’ayoyi da bayanai daban-daban a kansu. Marigayi Ayatullah Bahjat (R.A.) ya kuma yi wasu bayanai masu muhimmanci game da wannan rana da kuma yadda ya kamata a tunkare ta.

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, marigayi Ayatullah Bahjat (R.A.) ya yi magana kan ranar 9 ga Rabi’ul Awwal, ranar fara imamancin Imam Mahdi (A.J), inda ya bayyana wasu muhimman bayanai game da wannan rana da yadda ya kamata a gudanar da al’amuran da suka shafe ta.

Hujja ta fi gabatar da irin waɗannan majalisu muhimmanci!

Ayatullah Bahjat ya ce:

Malaman da suka kasance a zamaninmu, hatta wasu daga cikinsu sun kasance kamar sun riga zamaninsu, wasu mutane suna neman taimakonsu domin gudanar da abin da ake kira “Eid az-Zahra”. Wasu daga cikin malamai ba sa bayar da wannan taimako, yayin da wasu kuma suke bayarwa.

Ina ganin malaman addini, idan suna son yin wata hidima ga Ahlul-Baiti (A.S.) a wannan fanni na “Eid az-Zahra”, musamman ga masu son kafa hujja, abin da ya fi dacewa gare su shi ne su yi ƙoƙarin kawo hujja kan halifancin Amirul Muminin Ali (A.S.).

Hujjar ta kasance mai sauƙi, wacce ta ginu kan dalili, mai tabbatar da yaƙini, ta yadda idan aka gabatar da ita ga bango, kuma aka ba bangon damar yin magana, zai tabbatar da wannan magana ya ce: “Gaskiya tana tare da kai.”

Ni ina da cikakken yaƙini cewa masu ilimi da imani, idan suka yi ƙoƙarin nemo irin waɗannan hujjoji, za su same su.

Ba zagi ake buƙata ba, ba cin mutunci ba, ba tozarta wani ba; babu ɗaya daga cikin waɗannan da ake buƙata.

A maimakon haka, kafa hujja ya fi muhimmanci, kuma Allah ne kaɗai ya san mutane nawa ne hakan zai iya shigar da su cikin tafarkin gaskiya.

Mutane sun manta da cewa wannan shi ne abin da ya kamata a fara da shi. Daga cikin hujjoji guda goma da mutum ya tattara a tsawon rayuwarsa, Allah ne kaɗai ya san mutane nawa za su samu shiriya ta hanyar ɗaya daga cikinsu.

Me ya sa kuka yi watsi da wannan hanyar ta kafa hujja, alhali kuna mayar da hankali wajen shirya majalisu da sauran irin waɗannan ayyuka?

Ya kamata mu kula sosai, kada mu kauce daga hujja da dalili, kuma mu fahimci cewa hujja tana da wasu tasiri da waɗannan irin ayyuka ba su da shi.

Ko da a ce a cikin irin waɗannan ayyukan ma mutum zai iya yin wasu abubuwan da ba za su kasance abin ƙyama a wurin wasu ba, amma kafa hujja da dalili ya fi muhimmanci.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha